Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
#China70#Ana shirya wake-wake da raye-raye a Beijing don murnar cika shekaru 70 da kafuwar JJKS
2019-10-01 21:04:42        cri

A daren ranar 1 ga watan Oktoba ne, aka shirya wani gaggarumin bikin wake-wake da raye-raye a filin Tian'anmen dake nan birnin Beijing a wani bangare na shagulgulan murnar cika shekaru 70 da kafuwar Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin.

Gaggarumin bikin ya kunshi fannoni da dama, alal misali wake-wake da raye-raye, da wasan wuta, bikin da ya samu mahalartan dubun-dubata, wadanda suke rike da bangwayen hotunan bidiyo a hannayensu domin nunawa al'ummun kasa da kasa yadda Sinawa suka kafa sabuwar kasar Sin da kuma samun wadata. Sinawa kabilu daban daban da suka zo daga sassan fadin kasar sun yi raye-rayen kabilun gargajiya domin nuna farin cikinsu, gami da wasan wuta masu launuka iri iri suna tashi sama.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China