Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yarjejeniyar cinikayya cikin 'yanci ta Afirka na samar da karin damammaki na hadin gwiwa da Sin
2019-05-30 15:10:16        cri

Jakadan kasar Sin a kungiyar hadin kan Afirka ta AU Liu Yuxi, ya ce yarjejeniyar cinikayya cikin 'yanci ta nahiyar Afirka, na samar da karin damammaki ga kasashen nahiyar, wajen gudanar da hadin gwiwa da kasar Sin.

Jakada Liu ya ce, yarjejeniyar ta AfCFTA wadda ta fara aiki a yau Alhamis, za ta taimaka wajen fadada hada hadar cinikayya da kasar Sin. Kaza lika Sin na maraba da gina yankunan gudanar da cinikayya cikin 'yanci, za ta kuma tallafawa kasashen Afirka a fannin kara hade sassan su, tare da kokarin su na inganta gudanar wadannan yankuna.

Kasashen Afirka 22 ne dai suka amince da yarjejeniyar ta AfCFTA a watan da ya gabata, wanda hakan ya kai mafi karancin yawan kasashen da ake bukata domin fara aiwatar da ita.

Yarjejeniyar ta aza wani tubali na samuwar yankin cinikayya maras shinge irin sa mafi girma a duniya, idan aka yi la'akari da yawan kasashen da ke cikin ta, inda ta shafi mutane da yawan su ya haura biliyan 1.2, wanda kuma jimillar ma'aunin GDPn su ya kai dalar Amurka tiriliyan 2.5.

Da yake tsokaci game da hakan, Mr. Liu ya ce wannan mataki ya zamo ginshiki babba, da nahiyar Afirka ta kafa a 'yan shekarun baya bayan nan, a fannin dunkulewar ta, da bunkasa hadewar tattalin arzikin nahiyar. Jami'in ya kara da cewa, yarjejeniyar za ta ba da kafar zirga zirgar hajoji, da hidimomi, da kudade da ma al'umma ba tare da wani tarnaki ba, wanda hakan zai rage yawan haraji da shingen kasuwanni da a baya ake fuskanta, matakin da kuma zai yi muhimmin tasiri ga ci gaban tattalin arzikin nahiyar, tare da daga matsayin ta a fannin hada hadar cinikayya a mataki na kasa da kasa.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China