Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta bukaci Amurka ta rika aiwatar da furucinta kan sassautawa kamfanin Huawei
2019-08-20 09:50:50        cri

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, ta yi kira ga Amurka, ta aiwatar da furucinta kan sassauta haramtawa kamfanoninta sayar da kayayyaki ga katafaren kamfanin sadarwa na Huawei.

Kakakin ma'aikatar Geng Shuang, ya bayyana haka ne a jiya, bayan shugaban Amurka Donald Trump, ya bayyana a ranar Lahadi cewa, ba ya son kasarsa ta yi cinikayya da kamfanin Huawei na kasar Sin.

A cewar Geng Shuang, dangantakar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kamfanonin Sin da na Amurka, tana moriyar juna ce.

Ya kara da cewa, a lokacin da shugabannin kasashen biyu suka gana yayin taron kungiyar G20 a birnin Osaka cikin watan Yuni, Amurka ta yi alkawarin sahalewa kamfanoninta ci gaba da samar da kayayyaki ga kamfanin Huawei, yana mai kira ga Amurkar ta cika alkawarinta.

Har ila yau, ya ce lokaci da kuma yadda Amurka za ta cika alkawarinta, zai yi tasiri a kan mutunci da nagartarta, yana mai cewa, duniya na sa ido.

Kakakin ya ce, suna fatan Amurka za ta aiwatar da furucinta, ta kuma daina matsa lamba da kakaba takunkumin ba gaira ba dalili a kan Huawei da sauran kamfanonin kasar Sin, tare kuma da yi wa kamfanonin na Sin adalci. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China