Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bangaren Palasdinu ya yi Allah wadai da Isra'ila kan yadda ta sa aka shiga cikin masallacin Aqsa
2019-06-03 14:12:29        cri
Bangaren Palasdinu a jiya Lahadi ya yi Allah wadai da kasar Isra'ila kan yadda ta yarda da wasu Yahudawa su shiga cikin harabar masallacin Aqsa, wanda ke wani kebaben wurin da aka hana mutane shiga ciki na tsohon garin Jerusalem, yayin da aka kai karshen watan Ramadan.

Labarin da kafofin watsa labaru na kasar Isra'ila suka ruwaito jiya ya nuna cewa, 'yan sandan kasar sun ba Yahudawa damar shiga wannan yankin da aka kebe ne, don murnar "ranar birnin kudus", lamarin da ya janyo rashin gamsuwa, gami da zanga-zanga daga musulmai dake cikin birnin, har ma ya kai ga samun taho-mu-gama tsakanin Yahudawa da musulmai. Daga bisani 'yan sanda sun katse hanyar shiga cikin masallacin Aqsa na wasu sa'o'i. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China