Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta yi Allah wadai da zargin da ake mata na kasar dake sayarwa Amurka Fentanyl
2019-08-28 19:21:10        cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Geng Shuang, ya yi fatali da zargin da gwamnatin Amurka ta yi cewa, wai kasar Sin ta kasa dakatar da yadda ake sayar da maganin Fentanyl zuwa cikin Amurka, zargin da ya ce, babu kwararan shaidu kuma ba kamshin gaskiya a cikinsa.

Jami'in na kasar Sin ya bayyana hakan ne yayin taron manema labarai da aka gudanar a Larabar nan. Ya nanata cewa, har kullum gwamnatin kasar Sin tana dora muhimmanci kan kula da magunguna, da ma yaki da batutuwan da suka shafi magungunan da aka haramta.

A ranar 1 ga watan Mayun wannan shekara ne, kasar Sin ta sanya nau'o'in maganin na Fentanyl cikin jerin magungunan da aka haramta amfani da su a cikin kasar.

Geng ya ce, maganin ya samo asali ne a kasar Amurka ba kasar Sin ba. Idan kuma ana son a magance wannan matsala, ya kamata Amurka ta lalubo hanyoyin magance ta daga cikin gidanta. Ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin, a shirye take ta hada kai da sauran kasashe, ciki har da Amurka, don karfafa hadin gwiwar kasa da kasa kan yaki da nau'o'in maganin na Fentanyl, da karfafa ruhin kasar Sin da kara karfin takaita amfani da magunguna a duniya, da yaki da illar miyagun kwayoyi, ta yadda hakan zai amfani dukkan al'ummomin kasashe.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China