Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Manzon musamman na Xi zai ziyarci kasashen Afirka
2019-08-30 19:20:10        cri

A farkon wata mai zuwa ne, manzon musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, Yang Jiechi zai ziyarci kasashen Kenya da Najeriya da Saliyo, bisa gayyatar gwamnatocin kasashen.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Geng Shuang, shi ne ya sanar da hakan yau, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa.

A yayin ziyarar Yang, wanda har ila mamba ne a hukumar siyasa ta kwamitin koli na JKS, kana darektan ofishin hukumar harkokin wajen ta kwamitin koli na JKS, zai yi musayar ra'ayoyi da jami'an kasashen uku kan yadda za a bunkasa alaka tsakanin kasashen da sauran batutuwan kasa da kasa da na shiyya-shiyya dake shafarsu.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China