Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hanyar dogo tsakanin Abuja da Kaduna ta kasance hanyar dogo ta zamani "mai salon kasar Sin" ta farko a Afirka
2019-08-26 14:20:24        cri

Ranar 1 ga watan Octoba, rana ce ta bikin kasa ta kasar Sin, haka zalika, rana ce ta bikin samun 'yancin kai ta kasar Najeriya. Kasashen biyu na gudanar da hadin kai a fannoni daban daban yadda ya kamata, ciki har da shawarar "Ziri daya da hanya daya". A cikin wadannan manyan ayyukan hadin kai, hanyar dogo tsakanin Abuja da Kaduna ta kasance hanyar dogo ta zamani "mai salon kasar Sin" ta farko da ta soma aiki a nahiyar Afirka. A cikin shekaru uku da ta dauka ta na aiki, ta yi jigilar fasinjoji kusan miliyan 2, wadda ta zama wata muhimmiyar nasara da aka cimma kan hakikanin hadin kai a fannin manyan kayayyakin more rayuwa a tsakanin kasashen Sin da Najeriya.

Hanyar dogo ta Abuja da Kaduna ta hada kan Abuja, babban birnin kasar Najeriya, da Kaduna, muhimmin gari a fannin masana'antu a arewacin kasar, wadda tsawonta ya kai kilomita 186.5. Kuma ta kasance mataki na farko na ayyukan kafa hanyar dogo ta zamani ta kasar ta Najeriya. Gwamnatin kasar Sin ce ta ba da rancen kudi irin na gata, kuma kamfanin CCECC na kasar ne ya dauki nauyin ginawa tare kuma da ba da hidimar fasaha wajen gudanar da aikinta. Game da wannan aikin na hanyar dogon, kasar Sin ce ta tattara kudi, da yin tsare-tsare, da yin gine-gine, da kuma samar da na'urori, kana an gina hanyar dogon ne bisa ma'aunin kasar Sin, kuma kasar Sin ce ta samar da fasaha wajen gudanar da ayyukanta. Ana iya cewa, ita ce hanyar dogo ta zamani "mai salon kasar Sin" ta farko da ta soma aiki a nahiyar Afirka. A ranar 26 ga watan Yuli na shekarar 2016, shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, ya yanke kyalle don murnar kaddamar da hanyar dogon, kana ya hau jirgin kasa ta farko, hakan ya dora muhimmanci sosai kan wannan aiki. A ranar 26 ga watan Yulin bana, wato lokacin cika shekaru uku da soma gudanar da ayyukan na hanyar dogon ta Abuja zuwa Kaduna, kamfanin NRC na kasar Najeriya ya ba da lamba yabo ga sashen gudanar da ayyuka na kamfanin CCECC dake Najeriya, don gode masa kan goyon bayan da ya samar wa wannan muhimmiyar hanyar dogo.

A cikin shekaru uku da wani abu da suka wuce da aka soma gudanar da ayyukan hanyar dogo a tsakanin Abuja da Kaduna, an kyautata yanayin cunkoso a tsakanin birnin Abuja, jihar Niger da kuma ta Kaduna, hakan ya samar da sauki sosai ga fasonjoji wajen tafiye-tafiye. Ya zuwa yanzu, an riga an yi jigilar mutane kusan miliyan 2. Dan kasuwa Yusuf Mohammed, wanda kan hau jirgen kasa na hanyar dogon, ya ce,

"Yanzu ana samun sauyi kan hanyar sufuri ta jigilar fasinjoji da kayayyaki a nan kasar Najeriya, muna bukatar jiragen kasa da motoci masu yawa, don hada kan hedkwatan da jihohi daban daban kamar yadda ake yi a tsakanin Abuja da Kaduna. Muna bukatar hakan kwarai, ina fata kasar Sin za ta goyi bayanmu."

A ranar 21 ga watan Aflilu, sarki Idris Musa na yankin Jiwa na Abuja ya nada wani matashin kasar Sin sarautar "Wakilin Ayyuka", don yaba masa kan gudummowar da ya bayar wajen raya al'ummar yankin. Wannan matashi mai suna Kong Tao, shi ne babban daraktan sashen gudanar da ayyuka na kamfanin CCECC dake Najeriya, kuma ya kasance ya na aiki a Najeriya tsawon shekaru 9, kuma ya shiga cikin wasu manyan ayyuka da dama, ciki har da shimfida hanyar dogon tsakanin Abuja da Kaduna, da karamar hanyar dogo na zirga-zirgar jama'a ta Abuja da dai sauransu. Kong Tao ya bayyana cewa,

"A yayin da muke gina hanyar dogon da kuma gudanar da ayyukanta, mun yi hayar ma'aikata masu yawa na wurin, inda wasu suka yi aiki a fannin fasaha, musamman ma tsarin sarrafa inji na zamani. A shekarar da ta wuce kuma, mun aika da wasu daliban makarantar sakandare sama da goma zuwa kasar Sin, don su kara samun ilmi a jami'ar kasar. ana iya cewa, muna samar da gudummowa kan ci gaban fasahar wurin, a hakika dai muna kokarin raya al'umma mai kyakkyawar makoma ta kasashen Sin da Najeriya."

A cikin 'yan shekarun da suka gabata, an kammala manyan ayyuka guda uku, ciki har da hanyar dogo tsakanin Abuja da Kaduna, da karamar hanyar dogo na zirga-zirgar jama'a ta Abuja da kuma sabon babban ginin dake cikin filin jiragen sama na kasa da kasa daya bayan daya, a yankin na Jiwa. A matsayinsa na shugaban gargajiyar yankin, sarki Idris Musa ya ce,

"An cimma manyan nasarori kan hadin kai karkashin shawarar 'Ziri daya da hanya daya' a tsakanin kasashen Najeriya da Sin. Muna fatan ganin kamfanoni da hukumomin kasar Sin sun ci gaba da taimaka mana, don mu samu bunkasuwa a fannonin raya hanyar dogo ta zamani da dai sauransu."

A nasa bangaren, babban daraktan kamfanin CCECC dake Najeriya, Jiang Yigao ya bayyana cewa,

"Hanyar dogo tsakanin Abuja da Kaduna wata muhimmiyar nasara ce da aka cimma kan hadin kan shawarar 'Ziri daya da hanya daya' a tsakanin Sin da Najeriya. Nan gaba kuma, za a gina hanyoyin dogo masu yawa, jama'ar Najeriya za su samu hidimar hanyar dogo mafi kyau." (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China