Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Uganda ta bukaci a dauki matakan rage barazanar rashin tabbas game da tattalin arzikin duniya
2019-08-06 10:07:47        cri
Babban bankin kasar Uganda ya bukaci a dauki matakan rage barazanar rashin tabbas game da tattalin arzikin duniya a matakin shiyya.

Emmanuel Tumusiime Mutebile, gwamnan babban bankin kasar Uganda, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, yace koda yake, tattalin arzikin Uganda yana da karfi sosai kuma akwai yiwuwar zai iya karuwa da kashi 6.3 a bisa hasashen da aka yi na shekarar 2019/20, sai dai kamar sauran kasashen gabashin Afrika, kasar Uganda tana iya fuskantar kalubalolin tasirin dake da nasaba da matsalar tabarbarewar yanayin tattalin arzikin kasa da kasa.

Mutebile, wanda ya gabatar da jawabi a taron gwamnonin manyan bankunan na shiyyar wanda aka gudanar a makwabciyar kasar Rwanda, ya ce, hasashen matsakaici da dogon zango da aka yi game da makomar tattalin arzikin duniya yana cikin yanayin rashin tabbas.

A cewarsa, duk da irin jinkirin da ake samu wajen cimma hasashen da aka yi, hanya mafi muhimmanci da zata taimaka ya ta'allaka ne wajen aiwatar da shirin samar da kudaden bai daya na shiyyar kasashen gabashin Afrika wato (EAMU).

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China