Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanin Huawei dake Amurka ya kai kara ga ma'aikatar kasuwancin kasar
2019-06-23 15:46:52        cri

kwanan baya kamfanin Huawei na kasar Sin dake kasar Amurka ya kai kara ga ma'aikatar kasuwancin Amurka a kotun yankin musamman ta Washington, inda ya bayyana cewa, ma'aikatar kasuwancin Amurka ta tsara na'urorin kamfanin ba bisa ka'ida ba, har ba ta tsai da kuduri kan batun ba, matakin da ya sabawa doka.

Takardun karar da kotun ta nuna sun bayyana cewa, a shekarar 2017, kamfanin Huawei ya yi jigilar wasu na'urorin sadarwa wadanda aka kera su a kasar Sin zuwa wani dakin gwaji mai zaman kansa dake jihar California domin tantance su, daga baya yana son jigilar su zuwa nan kasar Sin bayan da aka kammala tantance su, amma a watan Satumban shekarar ta 2017, ma'aikatar kasuwancin kasar Amurka ta tsare wadannan na'urorin bisa dalilin gudanar da bincike kan batun game da ko ana bukatar neman iznin fitar da na'urorin zuwa ga kasar Sin a birnin Anchorage na jihar Alaska, kawo yanzu, watanni sama da 20 ke nan da suka wuce, amma ma'aikatar kasuwancin Amurka ba ta tsai da kuduri kan batun ba tukuna.

Kamfanin Huawei yana ganin cewa, ba a Amurka aka kera na'urorin ba, haka kuma ana jigilar su zuwa kasar inda a can ne aka kera su, babu bukatar a nemi izinin fitar da su zuwa kasar waje, a bayyane an lura cewa, matakin da ma'aikatar kasuwancin Amurka ta dauka ya sabawa dokar da abin ya shafa, a don haka kamfanin Huawei ya bukaci ma'aikatar ta tsaida kuduri kan batun a kan lokaci, idan ta tsaida kuduri cewa, jigilar da wadannan na'urorin bai sabawa doka ba, to ya dace ma'aikatar kasuwancin Amurka ta mayar da na'urorin ga kamfanin Huawei nan take.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China