Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanin Huawei zai ci gaba da kalubalantar umurnin hana shigo da na'urorinsa Amurka a gaban kotun kasar
2019-08-08 19:51:46        cri

Jiya Laraba 7 ga wata, agogon Amurka, hukumar kula da harkokin kwangilar gwamnatin kasar ta sanar da wani umunin wucin gadi, inda ta bayyana cewa, za ta hana hukumomin gwamnatin kasar sayan na'urorin sadarwa daga kamfanonin kasar Sin biyar, wadanda suka hada da kamfanin Huawei.

Dangane da wannan mataki, a yau kamfanin Huawei ya fitar da wata sanarwa ta kafofin watsa labarai, inda ya bayyana cewa, Amurka ta dauki matakin ne bisa "dokar tsaron kasa ta shekarar 2019" kawai, amma ba tare da shaidun cewa, kamfanin Huawei yana aikin da bai dace ba, sai don ta kuntatawa kamfanin tare kuma da ba da kariya ga kayayyakin kasar kanta.

A cikin sanarwa mai taken "gwamnatin Trump ta hana hukumomin gwamnatin Amurka su sayi na'urori hidimomin kamfanin Huawei" ya bayyana cewa, bai yi mamakin wannan labarin ba, amma umurni ne kawai na dokar tsaron kasar Amurka, kamfanin zai ci gaba da kalubalantar wannan batu a gaban kotun domin tantance ko umurnin ya dace da kundin tsarin mulkin kasar ta Amurka.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China