Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
'Yan sandan kasar Sin sun fara bincike bayan gano bindiga a cikin kunshin sako na kamfanin FedEx
2019-08-18 20:08:06        cri

'Yan sanda a Fuzhou dake lardin Fujian na kudu maso gabashin kasar Sin, sun bayyana a yau cewa, sun fara gudanar da bincike kan batun kunshin sako mai dauke da bindiga da kamfanin FedEx dauko.

Hukumar kula da tsaron al'umma ta yankin Jin'an ta ce ta samu rahoton cewa an ga bindiga a cikin wani kushin sako da wani daga Amurka ya aiko ta hannun kamfanin FedEx, zuwa ga wani kamfanin sayar da kayayyakin wasanni a Fujian.

Tuni rundunar 'yan sandan Fuzhou ta kwace bindigar tare da kaddamar da bincike kan batun. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China