Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tilas ne FedEx ya dauki matakai don tabbatar da moriyar masu amfani da hidimarsa na Sin
2019-07-26 14:13:35        cri
A kwanakin baya, hukumomin kasar Sin suka gabatar da bincike game da gazawar kamfanin FedEx na mika sako ga sunan wurin da aka rubuta, inda aka gano cewa, sanawar kamfanin FedEx ya fitar cewa, ya yi kuskure wajen mika wasikar kamfanin Huawei zuwa kasar Amurka ba shi da tushe, an ce, mai yiwuwa ne kamfanin FedEx ya hana shigar da abubuwan kamfanin Huawei fiye da 100 cikin kasar Sin da sauran ayyukan da ya gudanar ba bisa dokoki da ka'idoji ba.

Sabon binciken da aka yi, ya amsa kiran jama'a na gano hakikanin lamarin, wannan ya shaida imanin Sin na kare moriyar masu amfani da hidimar jigila bisa doka, da dauka matakai don nuna cewa, babu wani kamfani ko daidaikun jama'a dake kasar Sin, dake da ikon musammam, tilas kamfanin FedEx ya dauki matakai don tabbatar da kare moriyar masu amfana da hidimarsa a nan kasar Sin.

Sin tana maraba da kamfanonin kasashen wajen da suka raya ayyukansu a kasar, amma tilas ne su martaba dokokin kasar Sin da ka'idojin kasuwanci da kuma yarjejeniyoyin da suka cimma. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China