Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Zimbabwe ta yabawa Sin bisa taimakonta na horar da jama'a
2019-08-10 15:36:00        cri

Zimbabwe ta yabawa kasar Sin bisa damar da take ba jami'an gwamnatinta na samun horo, tana mai cewa, irin wannan taimako zai taimakawa kasar a kokarin da take na zama kasa mai matsakaicin kudin shiga ya zuwa shekarar 2030.

Shugaban sashen kula da kwarewar ma'aikata na hukumar kula da ma'aikatan gwamnatin kasar Zimbabwe, Moses Mhike ne ya bayyana haka, yayin liyafar ban kwana ga manyan jami'an gwamnatin kasar 25, wadanda za su halarci taron karawa juna sani kan kafatanin bangarorin tattalin arziki, da zai gudana a birnin Beijing daga ranar 12 zuwa 31 ga watan Agusta.

Tawagar jami'an 25 na daga cikin tawagogi da dama da jimilarsu ta kama 255, wadanda za su halarci irin wannan taro a kasar Sin a bana.

Shirya tarukan karawa juna sanin ya biyo bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna kan bunkasa kwarewar jama'a tsakanin Sin da Zimbabwe da aka yi a bara.

Karkashin yarjejeniyar, kasar Sin ta samar da gurabe 410 na horar da jami'an gwamnatin Zimbabwe a bara, da kuma wasu guraben 255 a bana.

Moses Mhike ya ce, an tsara shirye-shiryen ne ta yadda mahalarta za su fahimci ainihin ci gaban tattalin arzikin kasar Sin da koyo daga gogewar kasar a wannan fanni.

Ya ce, hukumar kula da ma'aikatan gwamnati ta kasarsa, na jinjinawa wannan kyakkyawan ci gaban, wanda ya dace da kiran gwamnati da shugaban kasar.

A nasa bangaren, Chen Ning, jami'in kula da batutuwan tattalin arziki da cinikayya a ofishin jakadancin Sin dake Zimbabwe, ya ce kasar Sin, za ta ci gaba da ba da damarmakin horo ga jami'an gwamnatin Zimbabwe domin taimakawa kasar a kokarinta na samun ci gaba. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China