![]() |
|
2019-08-09 09:47:20 cri |
A daya bangaren kuma, sakamakon binciken ya nuna hasashen raguwar karfin tattalin arzikin kasar a wannan shekara ta bana, inda bisa kiyasi, karuwar GDPn Amurka ba zai haura kaso 2.3 bisa dari ba a bana, adadin da ya yi kasa da na watan Yuli, wanda ya kai kaso 2.5.
Kaza lika masanan sun ce, ci gaban GDPn kasar zai hadu da tafiyar hawainiya zuwa kaso 1.8 bisa dari a watanni hudun karshen shekarar nan, sabanin kaso 3.1 bisa dari da aka samu a watanni 3 na farkon shekarar, da ma kaso 2.1 bisa dari da aka samu a tsakanin watannin Afirilu da Yunin shekarar ta bana.
Binciken jin ra'ayin masanan ya alakanta dukkanin wadannan koma baya, da matakin shugaba Donald Trump na ayyana karin harajin kaso 10 bisa dari, kan hajojin kasar Sin da ake shigarwa Amurka, wadanda darajar su ta kai kusan dalar Amurka biliyan 300. (Saminu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China