![]() |
|
2019-07-03 10:26:34 cri |
Hukumar ta ce, idan aka kwatanta da kudaden da suka shigo cikin kasar a rubu'i na 4 na shekarar 2018 da ta gabata, adadin kudade na baya-bayan da suka shigo cikin kasar daga waje ya kai kaso 216.03, karuwar kaso 34.61, idan aka kwatanta da na rubu'i na farko na shekarar 2018.
Adadin kudade mafi yawa da suka shigo cikin kasar a cewar hukumar ta NBS, ta same su ne ta hanyar takardun jari da na lamuni, wanda ya kai kaso 84.21 cikin 100 na jarin wajen da kasar ta samu a rubu'i na farko na shekarar 2019.
Wannan ya hada da sauran fannonin na zuba jari da suka tasamma kaso 12.91 cikin 100 da jarin kai tsaye na waje wanda ya kai kaso 2.86 cikin 100 na baki dayan jarin da ya shigo cikin kasar a shekarar 2019.
Hukumar kididdigar ta ce, ta samu wadannan alkaluma ne daga sashen tafiyar da harkokin mulki na babban bankin Najeriya, wanda hukumar ta tantance ta kuma amince da shi.(Ibrahim)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China