Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ma'aikatar harkokin cikin gidan Saudi ta yi gargadi game da jigilar maniyyata ba bisa ka'ida ba
2019-07-28 15:38:00        cri
Kamfanin dillancin labaran Saudi Press, ya rawaito ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar Saudiyyar tana gargadin direbobin tasi da na manyan motocin bus da su guji yin jigilar maniyyata ba tare da samun izini ba wajen daukarsu da nufin kai su wuraren gudanar da aikin ibada a birnin Makka.

Hukumomin kasar sun ce duk wadanda aka samu da karya doka za su fuskanci hukuncin zaman gidan yari na kwanaki 15 idan suka saba dokar a karon farko, da zaman watanni biyu idan suka saba dokar a karo na biyu, sai kuma hukuncin zaman yarin watanni 6 ga wadan suka karya dokar a karo na uku.

Ma'aikatar ta ce, za'a dinga rubanya hukuncin ne gwargwadon yadda aka kama wadanda suka saba dokar. Haka zalika hukuncin zai kuma shafi biyan tara da tusa keyar duk wani direba dan kasar waje a mayar da shi kasarsa.

Saudi Arabia tana daukar tsauraran matakai ne domin tabbatar da ganin an gudanar da aikin hajji cikin nasara da kuma kiyaye turmutsitsi a lokutan gudanar da ibadun aikin hajjin kana da samar da ayyukan hidama mafi inganci ga mahajjatan wannan shekarar. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China