Tamim Al-Dosary, jami'in ma'aikatar harkokin wajen kasar yace, ofisoshin jakadancin Saudiyya dake kasashen duniya daban daban da kuma ofisoshin wucin gadi na kasashen duniya da basu da ofishin jakadancin Saudiyya na dindindin a kasashensu, sun bayar da takardun visa kimanin miliyan 1 da dubu 720 da 680 kawo yanzu, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Saudi Press ya tabbatar da hakan.
Al-Dosary ya danganta samun takardun visar cikin sauki ne sakamakon ingantaccen tsarin fasaha da suka yi amfani da shi wanda yake iya sada ma'aikatar harkokin wajen kasar da ofisoshin jakadancin kai tsaye.
Ya zuwa jiya Alhamis, sama da maniyyata miliyan 1 da dubu 600 ne suka isa kasar mai tsarki domin gudanar da aikin hajjin bana.