in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Saudiyya ta sha alwashin dakile bullar cutuka a lokacin aikin hajjin bana
2018-08-01 10:56:36 cri
Kafar yada labaran kasar Saudi Al Arabiya ta rawaito hukumar lafiyar kasar Saudin ta tabbatar da cewa babu wata barazanar bullar cutar a lokacin aikin hajjin bana.

Aikin hajjin na wannan shekarar wanda za'a gudanar a tsakiyar watan nan na Augasta, an tsaurara matakan tsaro da kuma daukar matakan kare lafiyar mahajjata, in ji hukumar lafiyar.

Ma'aikatar lafiyar kasar mai tsarki tana bibiyar irin ci gaba da kuma sauye sauyen da ake samu game da sha'anin kiwon lafiya na duniya tare da yin hadin gwiwa da hukumar lafiya ta duniya WHO da sauran humumomin kiwon lafiya na kasa da kasa. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China