![]() |
|
2019-06-17 11:13:48 cri |
Kimanin mutane miliyan 4.2 ne suka samu horo a makarantun da kwalejojin a shekarar 2018 karkashin wani shirin bada horo ga al'umma, kamar yadda rahoton alkaluman yawan jami'ai da hukumar kula da ma'aikata ta kasar Sin na shekarar 2018 ya bayyana.
Yawan shirye-shiryen horas da sana'o'i da aka gudanar a duk fadin kasar a shekarar 2018 ya kai mutane sama da miliyan 16, wanda ya hada da wasu masu 'yan ci rani miliyan 8.3 da aka shigar da su ayyukan noma da kuma mutane miliyan 2.1 marasa aikin yi a yankunan birane da aka yiwa rijista. (Ahmad Fagam)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China