Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An binne wadanda suka mutu a hadarin tankar mai a Najeriya a kabarin gama gari
2019-07-04 09:43:02        cri

A ranar Laraba gwamnatin Najeriya ta dauki nauyin binne mutanen da hadarin fashewar tankar mai ya rutsa da su a kusa da wani kauye a shiyyar arewa ta tsakiyar Najeriya.

Al'amarin ya afku ne a ranar Litinin a kauyen Ahumbe dake jihar Benue, inda tankar mai ta fadi kana ta kama da wuta nan take, gomman mutane ne suka mutu a lokacin da suke kokarin kwasar man dake malala.

Kusan mutane 48 ne aka tabbatar da mutuwarsu, yayin da mutane 90 ke kwance a asibiti don karbar magani.

An binne wadanda suka mutu a rami guda yayin da mutane ke nuna jimami da zubar da hawaye a kusa da kauyen Ahumbe, inda lamarin ya faru a babbar hanyar Makurdi zuwa Aliade, karamar hukumar Gwer ta gabas dake jihar.

Mataimakin gwamnan jihar Benue, Benson Abounu, wanda ya jagoranci tawagar gwamnati a wajen jana'izar gama gari, ya ce, akwai mutane da dama da suka kone wadanda ba za'a iya gane kamanninsu ba.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cikin wata sanarwa cewe, ya yi matukar bakin ciki da hasarar rayukan da aka samu wadanda za'a iya kaucewa hakan.

Shugaban kasar ya bukaci jama'ar kasar ta yammacin Afrika da su dinga yin kaffa-kaffa game da ta'ammali da albarkatun mai domin gujewa irin wannan hasarar rayuka a nan gaba.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China