![]() |
|
2019-05-07 06:51:24 cri |
Kamfanin jirgin saman Afrika ta kudu (SAA) ya sanar da cewa, zai fara gudanar da jigilarsa ta kai tsaye daga birnin Johannesburg zuwa birnin Guangzhou na kasar Sin a watan Satumba.
Babban jami'in kamfanin jirgin saman na SAA, Vuyani Jarana, ya ce an tsara wannan mataki ne da nufin karfafa mu'amalar cinikayya tsakanin 'yan kasuwar dake sha'awar yin bulagulo a tsakanin biranen.
Jarana ya ce za'a dinga gudanar da zirga zirgar ne sau uku a cikin kowane mako, inda nisan tafiyar za ta kai sa'o'i 13 da minti 40, inda ake sa ran za'a samu tafiyar nisan zango mafi sauri ba tare da yada zango ba tsakanin manyan biranen biyu.(Ahmad Fagam)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China