Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta sha alwashin aiki tare da sauran sassa domin wanzar da zaman lafiya
2019-07-11 09:12:52        cri

Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Wu Haitao, ya ce kasar sa a shirye take ta yi aiki tare da kwamitin tsaron MDD, da sassan tawagogin 'yan sanda na kasashe masu ruwa da tsaki, da sakatariyar MDD, a fannin ayyukan wanzar da zaman lafiya ta MDD.

Wu Haitao ya bayyana hakan ne, yayin zaman kwamitin tsaron MDD game da hadin gwiwa tsakanin sassan uku. Ya ce Sin na fatan karfafa hadin kai tsakanin ta da kwamitin na tsaro, wajen inganta sadarwa, da yin aiki tare, domin kara kyautata nagartar ayyukan sassan uku.

Kaza lika, Sin za ta yi amfani da tasirin ta a fannin kwarewar sanin makamar aiki, ta hanyar tsara ayyukan wanzar da zaman lafiya, da baiwa dakarun dake aikin wanzar da zaman lafiya karin horo.

Wu Haitao ya kuma bayyana cewa, Sin na taka muhimmiyar rawa, a aikin wanzar da zaman lafiya na MDD, inda ya zuwa yanzu, sama da Sinawa masu aikin wanzar da zaman lafiya 2,500 ke ci gaba da wannan aiki a sassa 8 da ake gudanar da shi.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China