Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shirin yaki da ta'addanci na Sin muhimmin bangare ne na yakin da ake a duniya
2019-07-10 10:04:10        cri

Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Ma Zhaoxu, ya ce shirin yaki da ta'addanci da sauya halayyar masu tsatsauran ra'ayi na kasar Sin, muhimmin bangare ne na yakin da duniya ta ke da ta'addanci.

Da yake jawabi yayin muhawarar kwamitin sulhu na MDD kan barazanar tsaro da zaman lafiyar duniya, Ma Zhaoxu ya ce ayyukan ta'addanci sun shafi kasar Sin.

Ya ce, domin tunkarar barazanar ta'addanci da tsatsauran ra'ayi, kasar Sin ta dauki ingantattun matakan yaki da ta'addanci da sauya halayya ta hanyar doka, wadanda suka magance ayyukan ta'addanci a wurare daban daban, kuma suka ba da tabbaci ga hakkin samun ci gaba da kare rayuwar al'ummar dukkan kabilu.

Ya ce, shirin yaki da ta'adanci da sauya halayya na kasar Sin, ya dace da ka'idoji da dokokin MDD na yaki da ta'addanci da kare hakkokin bil adama.

Ma Zhaoxu, ya ce kasar Sin za ta ci gaba da yin musayar bayanai da kasa da kasa da kawancen kasashe, da kuma hada hannu da kasashe mambobin MDD, musammam kasashe masu tasowa, wajen yaki da ta'adannaci da manyan laifuffuka. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China