Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hauhawar farashin kayayyaki a Sin ya daidaita kan kaso 2.7 bisa dari
2019-07-10 15:10:24        cri

Hukumar kididdiga ta kasar Sin NBS, ta fitar da alkaluman kididdiga game da hauhawar farashin kayayyaki na CPI, wanda sakamakon sa ke nuna cewa, ya zuwa watan Yunin da ya gabata, hauhawar farashin kayayyaki a Sin, ya daidaita kan kaso 2.7 bisa dari a tsakanin shekara guda.

NBS ta ce, sakamakon mai alaka da hasashen kasuwanni, ya yi daidai da sakamakon fadadar kasuwanni cikin shekara daya ya zuwa watan Mayu. Kaza lika bisa alkaluman wata wata, kudaden sayayya a kasar sun yi kasa da kaso 0.1 bisa dari a watan da ya gabata.

A watannin farko na rabin shekarar nan, alkaluman CPI sun karu da kaso 2.2 bisa dari, idan an kwatanta da na makamancin lokaci na shekarar bara.

Da yake tsokaci game da haka, jami'i a hukumar ta NBS Dong Yaxiu, ya ce tasirin wasu abubuwa da suka gabata ne a baya, suka haifar da karuwar kaso 1.5 bisa dari na CPI a watan Yuni, yayin da sababbin yanayi suka ingiza karuwar kaso 1.2 bisa dari.

A daya hannun kuma, alkaluman da hukumar ta fitar a Larabar nan, sun nuna cewa, alkaluman farashin kayayyaki daga masana'antun samar da su ko CPPI a takaice, sun karu da kaso 0.3 bisa dari a watanni 6 na farkon shekarar nan ta 2019.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China