Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kashe 'yan sanda 4 a wani hari da aka kai ofishinsu a Nijeriya
2019-07-02 10:34:39        cri

An tabbatar da mutuwar Jami'an 'yan sanda 4, ciki har da babban jami'in guda, biyo bayan wani hari da wasu 'yan bindiga suka kai wani ofishin 'yan sanda a jihar Bayelsa dake kudancin Nijeriya.

A cewar kakakin rundunar 'yan sandan jihar Asinim Butswat, 'yan bindigar sun kutsa ofishin 'yan sanda na yankin Agudama-Ekpetiama dake Yanegoa babban birnin jihar, inda suka yi ta harbin kan mai uwa da wabi.

Wata majiya ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, babu wani farin hula da harin ya rutsa da shi, la'akari da cewa babu wani dake tsare a ofishin.

Majiyoyi da dama sun tabbatar da 'yan bindigar sun kuma sace harsasai da bindigogi da rigunan 'yan sanda

A cewar wata sanarwa daga hedkwatar rundunar, Babban Sufeton 'yan sandan kasar Mohammed Adamu, ya bada umarnin farautar maharan.

Ya kuma bada umarnin tura jami'an sashen tattara bayanan sirri don su taimakawa kokarin rundunar 'yan sanda jihar wajen gudanar da nasu bincike game da lamarin. (Fa'iza Msutapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China