Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Najeriya ya yi Allah wadai da harin da aka kai cibiyar 'yan gudun hijira dake Libya
2019-07-04 09:30:18        cri

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya a jiya Laraba, ya yi Allah wadai da kakkausar murya kan mummunan hari ta sama da aka kai kan cibiyar tsugunar da 'yan gudun hijira dake kusa da Tripoli, babban birnin kasar Libya.

Shugaba Buhari ya bayyana harin na ranar Talata da dare wanda ya kai ga halaka a kalla mutane 40 a matsayin rashin tausayi da rashin imani kan marasa galibu.

Buhari ya yi kira ga kasashen duniya da su gaggauta gudanar da bincike don zakulo wadanda suka kashe tare da jikkata 'yan gudun hijirar don ganin an hukunta su.

Shugaban ya ce, harin da aka kai, hannunka mai sanda ne ga sassan da ke fada da juna a Libya da ma al'ummomin kasa da kasa, da su hanzarta dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.

Kungiyar kula da kaurar jama'a ta duniya, ta bayyana a jiya Laraba cewa, akwai 'yan Najeriya da suka gamu da ajalinsu cikin mutane 40 din da aka kashe, sai dai ba ta bayyana adadin 'yan Najeriyar da suka mutu ba.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China