Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Noman Kayan Miya Na Taimakon Tattalin Arzikin Najeriya
2019-07-01 13:24:49        cri

Shugaban kungiyar sayar da kayan miya, wanda ke kula da kasuwancin bangaren tattasai a babbar kasuwar sayar da kayan gwari ta unguwar Mile 12 a jihar Legas, Dauda Sulaiman Tarai, ya ce noman kayan miya da manoman Arewa ke yi na taimaka wa Najeriya da al'ummarta baki daya.

Dauda Sulaiman, ya yi wannan bayani ne a ofishinsa da ke Mile 12, a lokacin da yake zantawa da wasu manyan manoman kayan miya daga Arewacin Nijeriya dake kai amfanin gonarsu Legas domin sayar wa al'umma.

Ya kara da cewa, a kokarin su na taimakawa noman rani da na damina, ya kamata gwamnatin kasar da na sauran jihohin Arewacin Nijeriya, su kara kaimi wajen bayar da tallafin noman kamar yadda suka saba a kowace shekara, domin kara wa manoman kwarin gwiwar noman rani da ta damina.

Ya ci gaba da yin kira gwamnatocin da su ci gaba da ba manoman tallafin takin zamani da kayan feshin kwari da sauran kayayyakin da manoman ke amfani da su a wajen noman ranin da na damina.

Sannan ya shawarci gwamnatocin da su bude kamfanonin da za a rinka sarrafa tattasai da tumatir domin ragewa manoman asara. (Leadership/Fa'iza)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China