Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yan Najeriya sun bukaci Buhari ya dauki sabbin matakan magance kalubalolin kasar a wa'adi na biyu
2019-05-30 09:57:07        cri

A jiya Laraba shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sha rantsuwar kama aiki yayin wani kwarya-kwaryar bikin rantsuwar da aka shirya don fara wa'adin mulkin shugaban kasar na biyu, sai dai wasu kwararru a kasar sun bukaci gwamnatin Najeriyar ta mayar da hankali wajen tabbatar da dora kasar wacce ita ce kasa mafi yawan al'umma a Afrika kan turbar ci gaba da kuma tabbatar da ingiza kasar zuwa mataki na gaba ta fuskar cigaba.

Akwai makoma mai kyau ga Najeriya, sakamakon yadda Allah ya huwacewa kasar albarkar yawan jama'a da kuma dunbun albarkatun kasa, amma sai dai akwai wasu kalubalolin da suka jima suna damun kasar wadanda suke bukatar a dauki sabbin matakai don magance su, in ji kwararrun.

Charles Onunaiju, wani mai sharhi ne kan al'amurran siyasa, ya bukaci sabuwar gwamnatin ta dauki matakan da za su haifar da samun kyakkyawan sakamako ga kasar.

Ya kamata a lalibo hanyoyin da Najeriyar za ta yi amfani da fasahar tunani wajen sarrafa arzikin kudadenta, a yi kokarin zuba makudan kudade, kuma a yi amfani da su domin fitar da mutane daga kangin fatara, sannan a dauki matakan hana barnatar da dukiyar gwamnati, wadanda galibi ake kashe kudaden kan manyan jami'an gwamnati da masu fada a ji, wadannan suna daga cikin hanyoyin da idan aka bi su za su sanya kasar da ma al'ummar kasar su kai mataki na gaba wato "next level" a turance, in ji mista Onunaiju.

Kunle Adeyemi-Doro, wani kwararren masanin kiwon lafiya dake zaune a birnin Legas, ya yi imanin cewa, dole ne sai an dauki muhimman matakai kafin a samu damar kyautatuwar yanayin zuba jari a kasar, akwai bukatar a dauki kwararan matakai ta fuskar inganta ilmi, da bunkasa aikin gona, da fadada hanyoyin samun tattalin arzikin kasar, wadannan suna daga cikin matakan da za su taimakawa Najeriyar wajen samun kyakkyawar makoma da kuma bunkasa rayuwar jama'ar kasar a nan gaba. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China