Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
'Yan Najeriya sun bukaci a sake fayyace dokokin hukumar sadarwar kasar bayan rufe wata kafar yada labaran kasar
2019-06-08 15:45:27        cri

'Yan Najeriya sun bukaci a sake fayyace ma'anar dokokin hukumar sadarwar kasar bayan da aka rufe wata shahararriyar kafar yada labarai a Najeriyar a kwanan nan.

Hukumar kula da kafafen yada labarai ta Najeriya (NBC), a ranar Alhamis ta bayar da umarnin rufe kamfanin sadarwa na Daar Communications, wanda ya mallaki gidan talabijin na (AIT), da gidan radiyon Raypower FM da kuma Faaji FM, bisa zargin kamfanin da taka dokokin yada labarai a lokacin da ya watsa wasu shirye-shiryensa.

Ana zargin kafar yada labaran da watsa wasu shirye shiryen nuna kiyayya, da yin kalaman dake raba kan al'umma, wanda hakan ya ci karo da tanade-tanaden dokokin hukumar ta NBC da ma dai an sha tuhumar kafar yada labaran da saba ka'idar hukumar tun shekaru biyu da suka gabata, darakta janar na hukumar NBC na kasar, Modibbo Kawu, shi ne ya bayyana hakan.

A cewar Kawu, maimakon kafar yada labaran ta yi sauye-sauye a shirye shiryenta, sai kawai ta yi gaban kanta ta yi amfani da kafar yada labaran wajen yada farfaganda wanda ya ci karo da tsarin hukumar sadarwar kasar.

Bayan dakatar da kafar yada labaran, wasu 'yan Najeriya da wasu kafofin yada labaran kasar, ciki har da kungiyar iditocin Najeriya, da kungiyar 'yan jaridu ta kasar, sun yi Allah wadai da matakin, inda suka bayyana matakin da cewa tamkar yin karan tsaye ne ga harkar yada labarai.

Masana da masu sharhi game da harkar yada labarai a kasar sun bukaci a kara fayyace dokokin hukumar dake sanya ido kan kafafen yada labaran Najeriyar NBC.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China