Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mayakan sa kai masu taimakawa jami'an tsaron Najeriya 1,000 sun mutu a yaki da Boko Haram
2019-06-20 10:43:34        cri
A kalla dakarun tsaro na farin na CJTF dake tallafawa jami'an tsaron Najeriya 1,000 ne aka hallaka a cikin shekaru 6 a fafutukar yaki da mayakan 'yan ta'adda na Boko Haram a shiyyar arewa maso gabashin kasar, kakakin kungiyar ta sabiliyan JTF ne ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua.

Jubril Gunda, kakakin kungiyar, kuma mai baiwa kungiyar ta CJTF shawara ta fuskar shari'a, ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a yayin wata tattaunawa a ranar Talata, ya ce alkaluman ya shafi daga shekarar 2013 zuwa 2019 ne.

CJTF, wacce aka kafa ta a shekarar 2013, ta kunshi kungiyoyin 'yan kato da gora daban daban wanda ya kunshi matasa da suka sadaukar da kansu don kare rayukan al'ummomin yankunansu, musamman a jihar Borno, inda can ne tushen kungiyar Boko Haram ta fara kaddamar da ayyukanta tun bayan wasu munanan hare-haren ta'addanci da kungiyar ta kaddamar babu kakkautawa a garin Maiduguri da sauran yankuna daga shekarar 2009.

Gunda ya ce, an kashe mayakan sa kai ne a lokacin da suke bakin daga don tallafawa jami'an tsaron Najeriya wajen yaki da Boko Haram. Kawo yanzu, ana zargin kungiyar ta Boko Haram ta hallaka mutane sama da 20,000, da raba mutane miliyan 2.3 da gidajensu a fadin Najeriya. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China