Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An samu gawar mutane 12 da suka mutu sanadiyyar fashewar bututun mai a Najeriya
2019-06-24 10:51:27        cri
Sama da gawawwaki 12 aka gano a wani wajen da bututun mai ya fashe a jahar Ribas mai arzikin mai, wata majiyar cikin gida ce ta bayyana rahoton.

An ji wata mummunar kara a wasu kayayyakin mai dake yankin Komkom na karamar hukumar Oyigbo a jahar Ribas a ranar Asabar, lamarin da ya firgita mazauna yankin.

An ga hayaki yana fita bayan mummunar karar, lamarin da ya ja hankalin hukumar bada agajin gaggawar yankin inda suka gargaza wajen domin kai dauki.

Jami'an 'yan sandan yankin sun ce, abu ne mai wahala su iya bayyana adadin mutanen da hadarin ya rutsa da su kawo yanzu, har sai sun kammala bincike.

Har yanzu ba za'a iya tabbatar da wanda ya mallaki kayayyakin man ba.

Kamfanin hakar mai na Shell ya ce, babu wasu alamu dake nuna cewa kayayykin aikin man kamfanin dake yankin Oyigbo ne suka fashe.

Haka zalika, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bada umarnin a gudanar da cikakken bincike game da lamarin, ya kara da cewa, ya yi matukar damuwa game da lamarin. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China