Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta yi kira da samar da na'urorin sanyaya yanayi ga kowa
2019-07-01 09:46:51        cri

Shugabar hukumar samar da makamashi mai dorewa ga kowa ta MDD Rachel Kyte, ta ce yayin da matakin zafi ya karu a duniya, samar da na'urorin sanyaya yanayi masu inganci da za su dore, kuma wadanda suka dace da raya muhalli na da muhimmanci ga harkokin yau da kullum.

Rachel Kyte, wadda kuma ita ce manzon musammam na sakatare janar na MDD kan samar da makamashi mai dorewa ga kowa, ta ce samar da na'urorin muhimmin batu ne na daidaito, kuma yayin da zafi ke karuwa, zai iya zama banbancin dake tsakanin rayuwa da mutuwa ga wasu.

Ta ce yayin da ake kara kaura zuwa birane, zafi da yawan al'umma na karuwa, tana mai cewa, sanyaya yanayin bukata ce ta gaggawa ta samun ci gaba, wadda kuma ke da tasiri kan yanayin duniya. Ta ce batun na bukatar mataki na gaggawa domin kare masu rauni, kana yana da muhimmanci wajen inganta ayyuka ta hanyar ba ma'aikata da manoma da dalibai damar gudanar da ayyukansu cikin kyakkyawan yanayi.

Har ila yau, Rachel Kyte, ta ce yayin da ake kara bukatar sanyaya yanayi, dole ne a tunkari kalubalen ta hanyar tsimin makamashi ko kuma a kara jefa rayuka da lafiya da ma duniya cikin hadari. Haka zalika, ta ce batun na samar da damarmakin kasuwanci ga 'yan kasuwa da kamfanonin dake tsarawa da kera na'urorin sanyaya yanayi masu inganci a kan farashi mai rahusa. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China