Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta yi kira a hada hannu domin taimakawa wadanda ayyukan ta'addanci suka shafa
2019-06-29 15:27:30        cri

Babban zauren MDD ya amince da wani kuduri a jiya, wanda ke kira ga dukkan mambobin majalisar, su samar da cikakken taimako ga wadanda ayyukan ta'addanci suka rutsa da su.

Kudurin, wanda aka amince da shi ba tare da kada kuri'a ba, na kira da a samar da shirye-shiryen magance dukkan bukatun wadanda ayyukan ta'addanci suka rutsa da su na matsakaici da dogon zango, da suka shafi rage musu radadi da sake tsugunar da su.

Kudurin ya yi kira ga dukkan mambobin majalisar, su yi la'akari da tasirin ayyukan ta'addanci a kan mata da yara, kana su kara tuntubar kungiyoyin kare mata da yara, yayin da suke tsara irin taimakon da za su ba su.

Ya kuma jadadda cewa, ya kamata a ba da taimakon ba tare da la'akari da cewa an gano ko hukunta wadanda ke da hannu a ayyukan ta'addancin ba.

Har ila yau, kudurin ya jadadda muhimmancin inganci da adalci da sahihancin tsarukan shari'a wajen taimakawa mutanen da ta'addanci ya rutsa da su. (Fa'iza Msutapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China