Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ya zuwa 2020 za a samu manyan motocin daukar fasinjoji a dukkan kauyukan kasar Sin
2019-06-12 09:43:45        cri

Ma'aikatar Sufuri ta kasar Sin, ta ce ana sa ran ya zuwa karshen watan Satumban 2020, dukkan kauyukan kasar Sin za su samu hidimar manyan motocin haya na daukar fasinjoji.

Kakakin ma'aikatar Wu Chungeng, ya shaidawa manema labarai cewa, sama da kauyuka 7,000 sun riga sun fara more hidimar a kowacce shekara cikin shekaru 5 da suka gabata, yayin da ma'aikatar ke inganta aikin ba tare da tangarda ba.

A cewar Wu Chungeng, har yanzu akwai kauyuka 10,000 da ba su samu hidimar manyan motocin haya ba. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China