Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
UNICEF ya yi tir da amfani da matasa a matsayin 'yan kunar bakin wake a Nijeriya
2019-06-19 09:24:28        cri

Asusun kula da kananan yara na MDD UNICEF, ya yi kira ga dukkan bangarorin dake rikici a yankin arewa maso gabashin Nijeriya, su daina kai hare-hare kan fararen hula, kuma su daina amfani da yara a cikin rikicin, sannan su kiyaye dokokin jin kai na kasa da kasa.

Cikin wata sanarwa da ta shiga hannun kamfanin dillancin labarai na Xinhua a Abuja, babban birnin kasar, wakilin UNICEF a Nijeriya, Peter Hawkins, ya ce tun daga shekarar 2012, kungiyoyi masu dauke da makamai a arewa maso gabashin Nijeriya ke horar da yara tare da amfani da su a matsayin 'yan kunar bakin wake, ko kuma mayaka ko jami'ansu, sannan sun yi wa mata fyade tare da tilastawa 'yan mata aurensu, baya ga wasu karin munanan laifuffuka da suka aiwatar a kan yaran.

A cewar sanarwar, take hakkin yara na baya-bayan nan da aka yi shi ne, amfani da su a matsayin 'yan kunar bakin wake, a yankin Madarari dake kusa da garin Konduga na jihar Borno da yammacin ranar Lahadin da ta gabata.

Akalla, mutane 30 aka kashe, yayin da wasu 42 suka raunana, a lokacin da suka tada bam dake jikinsu a cikin wani ayarin masoya kwallon kafa a wani gidan kallo da mashaya dake yankin. 'Yan mata 2 da yaro guda ne aka yi amfani da su wajen kai harin, kamar yadda kafafen watsa labarai na kasar da dama suka ruwaito.

Asusun UNICEF ya yi Allah wadai da harin cikin kakkausar kalamai, yana mai kira ga wadanda ke da hannu cikin rikicin su rika kare hakkokin yara a ko da yaushe.(Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China