Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yan Najeriya na burin ganin kyautatuwar dangantaka tsakanin majalisar zartaswa da ta dokoki
2019-06-12 10:24:24        cri

Bayan da aka kaddamar da majalisar dokokin Najeriya ta 9 a ranar Talata tare kuma da zabar sabbin shugabannin majalisar dattijai da ta wakilan kasar, 'yan Najeriyar sun bukaci a samu kyakkyawar dangantaka tsakanin bangaren zartaswa da na majalisun dokokin kasar domin ciyar da kasar gaba.

Majalisar dokokin da ta gabata ta sha yin takun saka tsakaninta da bangaren zartaswa, lamarin da ya yi sanadiyyar dakile ci gaban kasar a tsawon shekaru hudun da suka gabata.

Sanata Ahmed Lawan na jam'iyyar APC mai mulki shi ne ya zama sabon shugaban majalisar dattijai a majalisar ta 9, wadda aka kaddamar a birnin Abuja.

Haka zalika, Femi Gbajabiamila, mai wakiltar jihar Legas dake shiyyar kudu maso yammacin kasar, shi ne aka zaba a matsayin shugaban majalisar wakilan ta Najeriyar.

Dozie Ifebi, wani masanin tattalin arziki ne a Najeriyar, ya bayyana ra'ayinsa cewa, rashin jituwa tsakaninn jam'iyyun siyasar kasar har ma a tsakanin ita kanta jam'iyyar APC mai mulkin kasar sun taimaka wajen ruruta wutar rikici tsakanin bangarorin gwamnatocin biyu, wanda hakan na nufin rikici a wasu lokuta da dama yana iya yin tasiri wajen dakile ci gaban kasar a sanadiyyar takaddamar siyasar.

Majeed Bakare, wani mai sharhi kan al'amurran siyasa a Najeriyar ya bayyana makamancin wannan ra'ayi, yana mai cewa, ko da yake, bai kamata majalisun dokokin kasar su kasance 'yan amshin shata ba ga bangaren zartaswa, ya kamata 'yan majalisar su yi aiki da bangaren majalisar zartaswar kasar kan dukkan al'amurran da za su ciyar da kasar gaba.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China