Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Za a bada rancen kudi ga kasar Guinea don taimakawa mata wajen raya aikin noma da makamashi
2019-06-10 12:58:55        cri
Ma'aikatar kula da shirye-shirye da bunkasuwar tattalin arziki ta kasar Guinea ta bayar da labari a jiya cewa, za a gudanar da taron shekara-shekara na hukumar shugabannin bankin raya Afirka karo na 54 a birnin Malabo na kasar Equatorial Guinea tun daga ranar 11 zuwa 14 ga wannan wata. Ministar ma'aikatar shirye-shirye da bunkasuwar tattalin arzikin kasar Guinea Mme.Mama Kany Diallo za ta halarci taron a madadin gwamnatin kasarta.

Bisa yarjejeniyar da bankin raya Afirka da gwamnatin Guinea suka cimma, bankin raya Afirka yana shirin bada rancen kudi dala miliyan 535 ga gwamnatin Guinea tun daga shekarar 2019 zuwa 2022 don taimakawa kasar wajen raya aikin noma da makamashi. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China