in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Equatorial Guinea ya gana da Yang Jiechi
2019-01-18 09:55:24 cri

Jiya Alhamis, shugaban kasar Equatorial Guinea Teodoro Obiang Nguema Mbasogo, ya gana da wakilin musamman na Shugaban kasar Sin Xi Jinping, kana mamban hukumar siyasa ta kwamitin tsakiyar JKS Yang Jiechi a birnin Malabo, fadar mulkin kasar Equatorial Guinea.

A yayin ganawar tasu, Yang Jiechi ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da zurfafa mu'amalar dake tsakanin kasashen biyu, kan yadda ake gudanar da harkokin kasa, bisa ka'idar nuna gaskiya da adalci da shugaba Xi Jinping ya samar. Kuma tana fatan kasashen biyu za su nuna goyon baya ga juna, kan manyan batutuwan dake shafar moriyarsu. Kasar Sin tana son karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu bisa shawarar "Ziri daya da hanya daya", da kuma shirin "Manyan matakai takwas ta fuskar kara hadin gwiwar Sin da Afirka" da aka gabatar da shi a yayin taron kolin FOCAC da aka yi a birnin Beijing, ta yadda za ta ba da taimako ga kasar Equatorial Guinea, wajen neman bunkasuwa a fannoni daban daban, da tallafawa al'ummomin kasashen biyu, da kuma inganta dangantakar abokantaka dake tsakanin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare zuwa wani sabon matsayi.

A nasa bangare kuma, shugaba Mbasogo ya ce, kasar Sin muhimmiyar kawa ce ta hadin gwiwa da kasarsa, yana kuma godiya matuka dangane da goyon baya da taimakon da kasar Sin take baiwa kasar Equatorial Guinea cikin dogon lokaci. Kuma yana maraba da zuwan karin kamfanonin kasar Sin kasarsa don zuba jari, kuma yana sa ran karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu a lokacin da ake aiwatar da shawarar "Ziri daya da hanya daya", da kuma shirin "Manyan matakai takwas". (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China