Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ta'addanci: Sarkin Musulmi Ya Ce Sai Gwamnati Ta Dauki Matakai Bayan Addu'a
2019-06-05 20:42:56        cri
Mun samu labari daga shafin Leadershipayau na tarayyar Najeriya kan cewa, mai alfarma Sultan na Sakkwato, Muhammad Saíad Abubakar, ya yi la'akari da duk da cewa akwai bukatar tsananta addu'a daga sashen gwamnati a kowane mataki domin kawo karshen matsalar tsaro a kasar nan, amma sai ta dauki karin matakai baya ga hakan.

Basaraken, wanda ke nuna bakin cikinsa a kan yanda 'yan Nijeriya su ke yin hijirar dole daga gidajensu a sabili da matsalar tsaron, ya ce gwamnatoci a dukkanin matakai ya kamata su yi aiki tare domin magance matsalar.

A cewar shi, ba wata matsalar da ba za a iya magance ta ba, ya ce tare da mayar da hankali sosai, daukan matakai da adduíoíi matsalolin tsaron da kasar nan ke fuskanta za su iya zama tarihi. Ya yaba wa gwamnatin tarayya a kan yanda ta himmantu wajen magance matsalar, sai dai ya nanata kiran da ya yi a kan a samarwa da jamiían tsaro na kasar nan makaman da suka dace da zamani.

Ya kuma yi kira da a dage da yi wa shugabannin adduía domin su sami nasarar sauke nauyin da ke kansu. Basaraken wanda yake yin jawabin ga dimbin alíumma da suka taru a fadar na shi bayan hawan alíada na Hawan Sallah, ya kuma yi rokon Allah da Ya kunyatar da bukatar wadanda suke neman tauye Nijeriya, Ya kuma tona asirinsu da duk masu taimaka masu.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China