Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
CMG da jaridar Rasha sun kafa ofishin rubuta sharhi kan huldar dake tsakanin Sin da Rasha
2019-06-06 10:21:21        cri

 

Jiya Laraba a birnin Moscow, babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG da jaridar Rasha, wato jaridar mahukuntan Rasha suka kafa ofishin rubuta sharhi kan huldar dake tsakanin kasashen 2, inda Shen Haixiong, shugaban CMG da shugaban jaridar Rasha Pavel Negoitsa suka halarci bikin.

A cikin jawabinsa, Shen Haixiong ya ce, yayin da ake fuskantar manyan sauye-sauyen siyasa da tattalin arziki a duniya, shugabannin Sin da Rasha sun yi hangen nesa, wajen kara azama kan raya huldar abota da hadin gwiwa dake tsakanin kasashen 2 daga dukkan fannoni bisa manyan tsare-tsare a sabon zamani. Sa'an nan kafofin yada labaru na kasashen 2 suna tuntubar juna, da amincewa juna, da taimakawa juna, a kokarin bada taimako wajen raya huldar dake tsakanin kasashen 2 daga sassa daban daban da yada labaru masu adalci a duniya.

A nasa bangaren, Pavel Negoitsa ya ce, jaridar Rasha ta dauki tsawon shekaru tana hada kai da CMG. Kafuwar ofishin rubuta sharhi kan huldar dake tsakanin kasashen 2 ta alamta cewa, bangarorin 2 sun samu muhimmin ci gaba a fannin hadin kai.

CMG da jaridar Rasha zasu bada muhimmanci wajen raya shirin sharhi kan huldar dake tsakanin Sin da Rasha, inda za a rubuta sharhi cikin hadin gwiwar bangarorin 2 dangane da ziyarar juna ta shugabannin kasashen 2, cika shekaru 70 da kulla huldar jakadanci tsakanin kasashen 2, hadin kan shawarar "ziri daya da hanya daya" da kawancen tattalin arzikin Turai da Asiya, da manyan batutuwan dake tsakanin Sin da Rasha, a kokarin yin cikakken bayani kan ci gaban huldar abota da hadin gwiwa tsakanin kasashen 2 daga dukkan fannoni bisa manyan tsare-tsare a sabon zamani da sa ido kan sabbin ci gaban hadin gwiwarsu. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China