2019-05-14 20:20:00 cri |
Kasar Sin ta musunta zargin da aka yi mata wai ta karya alkawarin da ta dauka yayin da take yin tattaunawa kan tattalin arziki da cinikayya tsakaninta da Amurka.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Geng Shuang shi ne ya bayyana hakan a yayin taron ganawa da manema labaran da aka saba yi a nan birnin Beijing, yana mai cewa, idan an kalli sakamakon da aka samu tun bayan da sassan biyu suka yi tattauawa har sau 11, za a ga kasar da ta karya alkawarin da ta dauka. A watan Mayun bara, sassan biyu sun taba cimma matsaya da dama kan batun tattalin arziki da cinikayya, har sun gabatar da wata hadaddiyar sanarwa a Washington, amma bayan wasu 'yan kwanaki kawai, sai Amurka ta canja ra'ayinta, har ta karya alkawarin da ta dauka. A watan Disamban bara kuma, sassan biyu sun cimma matsaya kan adadin sayayya tsakaninsu, amma ba da dadewa ba sai Amurka ta daga farashin kayayyaki a cikin tattaunawar da suka yi kamar yadda take so, a don haka ana iya cewa, bai kamata ba a ce kasar Sin ta karya alkawarin da ta dauka.
Geng Shuang ya jaddada cewa, kasarsa tana fatan Amurka za ta hada kai tare da kasar Sin, ta yadda za su daddale wata yarjejeniyar moriyar juna bisa tushen martabar juna da daidaito da kuma cika alkawarin da suka dauka.(Jamila)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China