![]() |
|
2019-05-17 10:21:00 cri |
Gao ya bayyana hakan ne a jiya Alhamis, biyowa bayan sanarwar ma'aikatar harkokin cinikayyar Amurka, wadda ta sanya kamfanin Huawei da abokan huldar sa, cikin jerin kamfanonin da sashen lura da masana'antu da tsaron kasar Amurka suka yiwa shingen ma'amala da kamfanonin ta a fannin hana saya ko musayar fasahohi da kamfanonin Amurka.
Jami'in na Sin ya ce har kullum, kasar sa na umartar kamfanonin ta da su kiyaye dokokin wuraren da suke hada hada cikin su, da dokokin hada hadar fitar da hajoji, su kuma kare dokokin kasashen da suke hulda da su.
Daga nan sai Gao ya yi kira ga Amurka, da ta dakatar da aiwatar da manufofi marasa dacewa, ta rungumi matakan gudanar da kasuwanci da hadin gwiwa tsakanin kamfanonin kasashen biyu, domin kaucewa kara tsanantar yanayin kawancen tattalin arziki da na cinikayya tsakanin kasashen biyu. (Saminu)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China