![]() |
|
2019-05-27 11:08:10 cri |
Victor Kisob, ya ce sassa masu zaman kan su na da kwarewa a fannin gudanar da bincike, da samar da ci gaba da kirkire kirkire, domin samar da ci gaba mai dorewa a birane.
Kisob ya bayyana hakan ne a jiya Lahadi, yayin taron masu ruwa da tsaki da jagororin 'yan kasuwa, gabanin taron farko na MDD game da kula da muhallin halittu da za a bude a yau Litinin. Ana sa ran taron na yau, zai hallara wakilai 3,000 daga kasashe mambobin MDD 193.
Da yake tsokaci game da yawaitar bude sabbin birane da kalubalen dake tattare da hakan, Kisob ya ce ya zama wajibi a samar da dabarun samar da ababen more rayuwa masu dorewa da ake bukata ga mazauna birane.
Jami'in ya ce hukumar UN-Habitat na da burin tabbatar da cin cikakkiyar gajiyar sabbin dabarun kirkire kirkire masu dorewa a birane.
Mr. Kisob ya kara da cewa, birane masu kunshe da shuke shuke, za su tallafawa kasashen duniya, wajen cimma burin aiwatar da yarjejeniyar Paris ta sauyin yanayi. (Saminu Alhassan)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China