![]() |
|
2019-05-17 10:54:40 cri |
Chen Xu ya bayyana haka ne a jiya, yayin da yake mika takardar aikinsa na sabon wakilin kasar Sin ga Darakta Janar na ofishin MDD a Geneva, Micheal Moller.
Da yake bayyana Geneva a matsayin daya daga cikin cibiyoyin huldar diflomasiyya ta kasa da kasa mai muhimmanci, Chen Xu ya ce martaba huldar kasa da kasa buri ne na yawancin kasashen duniya, kuma a shirye tawagar kasar Sin a Geneva take, ta yi aiki da ofishin wajen inganta dangantaka da karfafa hadin kan kasa da kasa tare da bada gudunmuwa ga gina al'umma mai kyakkyawar makoma.
A nasa bangaren, Micheal Moller, ya bayyana amincewarsa da sabon wakilin na kasar Sin, yana mai cewa, duniyar yanzu na bukatar huldar kasa da kasa, kuma muhimmancin Geneva a matsayin cibiyar huldar diflomasiyya tsakanin kasashe na karuwa.
Ya kuma shaidawa Chen Xu cewa, MDD na bada muhimmanci ga matsayin kasar Sin, kuma ta na yabawa irin gudunmuwar da take bayarwa ga karfafa tsarin huldar kasa da kasa. (Fa'iza Mustapha)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China