in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata masu fama da radadin ciwon sankara su mai da hankali kan shan maganin sassauta radadin ciwon yadda ya kamata
2020-10-14 08:44:37 cri

Ranar 11 ga watan Oktoban ko wace shekara, rana ce ta sassauta radadin ciwo. Radadi ko zafin ciwon sankara, yana daya daga cikin wahalhalun da masu kamuwa da cutar sankara suke fama da su. Yana addabar dimbin masu fama da cutar sankara da ta kai matsayin da babu magani, har ma ba su iya jurewa. An yi karin bayani da cewa, kamata ya yi masu fama da radadin cutar sankara su mai da hankali kan shan maganin sassauta radadin cutar yadda ya kamata, ta yadda za su samu jinya ta hanyar kimiyya.

Alkaluman hukumar kiwon lafiya ta kasa da kasa wato WHO sun nuna cewa, fiye da rabin masu fama da cutar sankara da ta kai matsayin da babu magani suna fama da zafi, sa'an nan wasu kashi 30 cikin kashi 100 ne suke fama da tsananin zafi. A kasar Sin kuma, a ko wace rana masu fama da ciwon sankara kimanin miliyan 1 suna yaki da wannan matsala, amma a cikinsu, kashi 30 cikin kashi 100 ne kawai aka samu nasarar rage radadin ciwon da suke fama da shi.

Wasu masu ba da magani da ke aiki a asibitocin jiyyar cututtukan sankara a kasar Sin sun yi bayani da cewa, kullum masu fama da ciwon sankara ko kuma dangoginsu su kan yi tambaya kan yadda suke shan maganin sassauta radadin ciwon. Wasu ba su san irin wannan magani sosai ba, kana kuma ba su san yadda suke shan irin wannan magani yadda ya kamata ba.

Alal misali, wasu nazarce-nazarce sun tabbatar da cewa, shan maganin Aspirin da Fenbid na dogon lokaci kan yi illa ga zuciya, da sassan jiki masu narkar da abinci da ma koda. Har ila yau kuma an kayyade yawan irin wadannan magunguna mafi yawa da ya kamata a sha. Idan an sha irin wadannan magunguna fiye da yadda aka kayyade, to, hakan ba zai kai ga kara rage radadin ciwo ba, a maimakon haka ma, barazanar da za a fuskanta wajen illanta lafiya za ta karu kwarai da gaske. Don haka idan masu fama da radadin ciwon sankara suna bukatar shan maganin rage radadin ciwon na dogon lokaci, to, maganin Morphine da dangoginsu, sun fi dacewa ga lafiyarsu.

Ban da haka kuma, wasu suna ganin cewa, bai dace a sha maganin Morphine da yawa ba, saboda akwai yiwuwar illa da ke tattare da shan maganin. A zahiri, ga masu koshin lafiya, shan maganin na Morphine iya zama jiki, amma zafin da masu fama da radadin ciwon sankara suke fama da shi ba zai yi wani tasiri a jikinsu ba. Idan masu kamuwa da ciwon sankara sun sha maganin Morphine don rage radadin ciwon bisa shawarar likita, to, shan maganin ba zai zama jiki ba, ba za su dogaro da maganin ba.

Haka zalika masu kamuwa da ciwon sankara da yawa suna ganin cewa, idan ba sa jin zafi, to, ba sa bukatar shan maganin rage radadin ciwo ko kuma su rage yawan maganin da suke sha. Hakika dai, idan ba su sha maganin kamar yadda likitoci suka fada ba, to, maganin ba zai yi aiki yadda ya kamata ba, yayin da zafin ya karu ko kuma aka fara jin zafi. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China