in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ta yaya za a taimaka kananan yara da aka kuna a fatarsu cikin gaggawa?
2020-08-10 09:52:57 cri

Lokacin zafi, lokaci ne da aka fi samun lalacewar fata sakamakon kuna, musamman ma kananan yara. Madam Zhang Chuji, wata likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta yi karin bayani da cewa, idan kananan yara suka kona fatarsu ba zato ba tsammani, ya zama tilas a ba su ceton gaggawa daga fannoni guda 3, wato nisantar da su daga abun da ya kona su, wanke fatar da ya kone da ruwa mai sanyi har na mintoci 30 ko fiye da haka, sa'an nan a kai su asibti don ganin likita cikin sauri.

Bari mu yi karin bayani kan wadannan fannoni 3. Da farko, nisantar da kananan yara daga abun da ya kona su. Mutanen da suke kusa da kananan yara, ya kamata su tabbatar da tsaron lafiyarsu tukuna, sa'an nan su cire ko yanke tufafin da yaran suke sanya da shi cikin hanzari, tare da kawar da abu mai zafi da ke kan fatar yaran, da kuma daga wayar wutar lantaki da sandar katako, a kokarin rage zafin da yaran suke ji a fatarsu. Har ila yau kuma, kada a yaga tufafin kananan yaran da karfi, kuma kada a soki bororo ko kuma yaga bororon dake kan fatar yaran.

Na biyu kuma, nan da nan ba tare da bata lokaci ba a wanke fatar kananan yara da ya kone da ruwan sanyi har na mintoci 30 ko fiye da haka. Kada a dogaro da wasu hanyoyin gargajiya, alal misali, a shafa miya ko maganin goge hakora kan fatar da ya kone, wanda zai sake raunana kananan yaran.

Na uku kuma, a kai kananan yara asibiti don ganin likita cikin hanzari. Tsarin fatar yaro ba shi da karfi, shi ya sa idan suka kone, raunin da su kan yi ya fi na baligai tsanani. Kamata ya yi a kai su asibitin da ke kusa don likita su ba su jinyar gaggawa, kada a bata lokaci, in ba haka ba, ruwan jikinsu zai kare, kwayoyin cuta su shiga fatar da ya kone, har ma wasu kananan yara su suma, su rasa rayukansu a karshe.

Bisa kididdigar da aka samu, an ce, kuna ta zama na biyu cikin dalilan da suke haddasa kananan yara jinya a asibiti sakamakon raunin da suka ji. Madam Zhang Chuji ta yi mana gargadi da cewa, yiwuwar konewar kananan yara a cikin daki ta fi yiwuwar konewa a wajen daki yawa. A cikin gida, wurin cin abinci, wurin dafa abinci, wurin wanka, wurin karbar baki, su ne wuraren da kananan yara kan kone. Kananan yaran da suka kone da yawansu ya kai kashi 75 cikin kashi dari, su ne wadanda shekarunsu ba su kai 3 a duniya ba, kuma wasu kashi 15 cikin kashi dari sune wadanda shekarunsu suka wuce 3 amma ba su kai 8 ba. Iyaye da kuma mutanen da ke kulawa da kananan yara kamata ya yi su kara mai da hankali kan abubuwan da suke iya kona kananan yara, su kuma ilmantar da kananan yara da ba su fara karatu a makaranta ba, haka zalika, su koyi yadda za a taimakawa kananan yaran da suka kone ta hanyar da ta dace, a kokarin kare su daga sake jikkata. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China