in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bayanan masana game da fa'idar cin abinci a kimiyance ko bisa yadda jama'a ke tunani (C)
2019-11-28 17:23:54 cri

Akwai wasu kyawawan fasahohi da aka gada daga zuriya zuwa zuriya dangane da cin abinci. Masana kan abubuwa masu gina jiki suna ganin cewa, wasu ra'ayoyin da aka dade ana dogara a kansu da ake amfani da su. Ko mun amince da wadannan rashin fahimta ko a'a? Masu nazari daga kasar Amurka sun yi nazari kan wasu bayanai da aka baza dangane da amfanin abinci don tabbatar da gaskiyar wadannan bayanai ko kalamai.

Shin cin karas yana iya karawa mutum ganin abu? A'a, ba haka ba ne. Masu nazarin sun yi karin bayani da cewa, hakika karas yana cike da bitamin A, wanda yake taimakawa wajen tabbatar da lafiyar idanun mutane. Amma ba a ce, karas shi kadai yana iya karawa mutane ganin abu ba.

Baya ga karas, kayayyakin madara, kwai, kifi da hantar dabbobi su ma suna cike da bitamin A. Haka zalika kuma, peach, tumatir, alayyaho, nau'in kabeji, farin kabeji da wasu 'ya'yan itatuwa da kayayyakin lambu suna taimakawa lafiyar idanun mutane. Masu nazarin sun kara da cewa, cin abincin da ke kushe da dukkan sinadaran gina jiki da yin rayuwa ta hanyar da ta dace suna iya taimakawa lafiyar idanu, amma ya zuwa yanzu ba a gano wani nau'in abinci da ya fi taimakawa ido ba.

Shin cin abubuwa masu yaji yana haddasa gyambo ga kayayyakin jiki masu narkar da abinci? A'a, ba haka ba ne! Abubuwa masu sinadarin Acid su ne suke haddasa gyambo ga kayayyakin jiki masu narkar da abinci, ba abubuwa masu yaji ba. Masu nazarin sun yi bayani da cewa, wani nau'in kwayoyin cuta ne suke haddasa yawancin gyambo ga kayayyakin jiki masu narkar da abinci, kuma magunguna kamar Aspirin suma suna haddasa wasu nau'o'in gyambon ciki.

Amma me ya sa ake tsammani yaji, kori, da wasu abinci masu yaji su ne suke haddasa gyambon ciki? Masu nazarin sun yi bayani da cewa, abinci masu yaji kan sa tumbi ya yi zafi har ma ya yi ciwo. Idan mutum ya ci abinci mau yaji, ya kan ji tumbinsa yana ciwo, sai ya yi tsammani ya gamu da gyambon ciki, wasu likitoci ma su kan ce, majiyyata sun gamu da gyambon ciki. Amma hakika ba haka ba ne. Amma haka lamarin yake, matsin lambar da ake fuskanta da kuma giya ba su haddasa gyambon ciki

Ko da yake a shekarun 1980 an tabbatar da cewa, kwayoyin cuta ne suka haddasa gyambo ga kayayyakin jiki masu narkar da abinci, amma ya zuwa yanzu ana jita-jita cewa, abinci masu yaji sune suke haddasa gyambon ciki. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China