lafiya1901.m4a
|
Masu nazari daga jami'ar Southern California ta Amurka sun tantance bayanan lafiyar kananan yara kusan dubu 2 da dari 2 wadanda shekarunsu suka wuce 5 amma ba su kai 9 ba. Yayin da ake nazarin lafiyar wadannan yara, ba su fuskanci matsalar kiba ba, amma wasu daliban kimanan kashi 13.5 cikin dari ne suke fama da ciwon asma. Masu nazarin sun dauki shekaru 10 suna nazari kan yaran. Yayin da aka kammala nazarin, kashi 1 cikin kashi 6 daga cikin wadannan yara ne suke fama da matsalar kiba. An nuna cewa, in an kwatanta da wadanda ba su kamu da ciwon asma ba, kananan yara da suka taba kamuwa da asma sun fi yiwuwar gamuwa da matsalar kiba, milisa da kashi 51 cikin dari.
Masu nazarin sun yi bayani da cewa, idan alamun ciwon bai ragu a jikin kananan yara masu fama da asman ba, hakan na iya kawo cikas ga yadda suke motsa jiki, sa'an nan kuma mai yiwuwa ne shan magungunan Hormone cikin dogon lokaci zai haddasa gamuwa da matsalar kiba. Duk da haka ba a san ainihin dalilin da ya sa ciwon asma ya ke haddasa matsalar kiba ba. Akwai butakar masana su kara yin nazari a nan gaba.
Da ma likitoci suna muhawara kan alakar da ke tsakanin matsalar kiba da ciwon asma. Yawancin nazarce-nazarce da aka yi a baya sun mai da hankali kan yiwuwar kamuwa da ciwon asma sakamakon samun kiba. Akwai kuma nazarce-nazarce kalikan dangane da yiwuwar samun kiba sakamakon kamuwa da ciwon asma, musamman ma kamuwa da ciwon a lokacin yaranta.
An raba magungunan dake maganin ciwon asma zuwa kashi 2, wato maganin sassauta alamun ciwon cikin hanzari, da kuma maganin shawo kan ciwon na dogon lokaci.
Masu nazarin sun gano cewa, maganin sassauta alamun ciwon cikin hanzari yana iya rage yiwuwar yin kiba da kashi 43 cikin dari. Amma ba a san dalilin da ya sa haka ba tukuna.
Masu nazarin na Amurka sun nuna cewa, nazarinsu yana da ma'ana sosai wajen bayyana muhimmancin tabbatar da wani karamin yaro ko wata karamar yarinya ta kamu da ciwon asma ko a'a, yin rigakafin kamuwa da ciwon, da riga kafin alamun ciwon. Haka zalika kuma, yin rigakafi da kuma hana kananan yara kamuwa da ciwon asma, suna da muhimmanci sosai wajen kare mutane daga yin kiba da kuma illar da sauran cututtukan dake addabar mutane sannu a hankali suka yi sakamakon yin kiba (Tasallah Yuan)