in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Matakan Karfafa Kasuwannin Gida Za Su Taimaka Ga Bunkasar Tattalin Arzikin Kasar Sin
2019-01-27 20:11:43 cri
Zuwa ga sashen Hausa na CMG.

Tare da fatan daukacin ma'aikatan sashen Hausa na babban rukunin gidan rediyo da telibijin na kasar Sin (CMG) suna cikin koshin lafiya a birnin Beijing kamar yadda nake a nan birnin Tianjin. Da farko, ina yi muku godiya bisa dama da kuka ba ni domin na tofa albarkacin bakina dangane da sauye sauye da kasar Sin ta fara aiwatarwa da nufin habaka kasuwannin cikin gida tare da kara bude kofofinta ga kasashen waje, sakamakon sauyi da kuma karuwar rashin tabbas daga kasuwannin kasa da kasa.

Ba shakka, shugabannin kasar Sin karkashin JKS sun yi fice wajen hanzarta daukan duk wasu matakai da suka dace wajen tallafar tattalin arziki da kara kyautata rayuwar al'umma a lokacin da ya dace wato ba tare da wani jan kafa ba. Kamar yadda Bahaushe kan ce, "Da zafi-zafi a kan bugi karfe." Kuma akwai kyakkyawan zato cewa wadannan matakai da gwamnati ta bullo da su, kwalliya za ta biya kudin sabulu, wato tattalin arziikin kasar Sin zai ci gaba da samun tagomashi sannu a hankali.

A 'yan shekarun nan, kasar Sin ta cimma manyan nasarori ta fannoni da dama tun daga sha'anin tattalin arziki, zuwa bunkasar kirkire kirkire, da karuwar tallafin da take bayarwa ga nahiyar Afirka kai da ma gudunmawa wajen habaka tallafin arzikin duniya baki daya. Hakika wadannan manyan nasarori sun kawo hassada da nuna adawa a fakaice daga yammacin duniya musamman kasar Amurka wadda a halin yanzu adawarta da kuma kokarin ganin cewa ta dakushe bunkasuwar kasar Sin ta kowane hali ya bayyana a fili, duba da yadda Amurka ke son fakewa da guzuma wajen harbin karsana, inda ta fake da batun takaddamar ciniki wajen kawo illa ga ci gaban kasar Sin. A yanzu dai, hassada da kasar Amurka ke yi ga kasar Sin ta riga ta fito fili bayan da aka jiyo shugaba Trump a karo da dama yana dora alhakin koma bayan tattalin arzikin kasarsa a kan Sin. Matakan ramuwar gayya da hukumomin Beijing suka dauka kan kayayyakin da ake shigo da su daga Amurka ya yi daidai kuma tauna aya ne domin tsakuwa ta ji tsoro. Ban da Amurka, wasu kasashen yammacin duniya su ma sun bullo da wani sabon salo na hanawa ko takaita shigar kayayyakin kasar Sin cikin kasuwannin kasahensu. Hakika, wannan rashin adalci ne domin kayayyakin kasar Sin suna da farin jini da karbuwa a kasuwannin duniya ne saboda saukin farashinsu, kuma a zahiri ba bu wata kasa a duniya da za ta iya samar da kayayyakin da suka dara na kasar Sin rahusa. A ra'ayina, duk kasar da ta dauki matakan hanawa ko takaita yawan kayan da kasar Sin ke shigarwa kawai tana cutar da al'ummarta ne ta hanyar tilasta musu sayen masu tsada.

Masu iya magana kan ce, "Idan hagu ta ki sai a koma dama." Ba shakka, ina da yakinin cewa wadannan matakai na mayar da hankali wajen habaka kasuwannin cikin gida da mahukunta suka fara dauka za su cimma nasara wajen cike gibin cinikin ketare. Duba da cewa kasuwar gida ta Sin ita kadai wata hamshakiyar kasuwa ce bisa la'akari da dimbin al'ummar Sinawa wanda ya zarce na daukacin al'ummar nahiyar Afirka. Hakika, na yi nazarin matakan daki-daki kamar yadda mataimakin shugaban kwamitin raya kasa da gyare-gyare na kasar Sin Mr. Ning Jizhe, ya bayyana. Lalle rage kudaden haraji game da bayar da basussuka masu rangwamen ruwa ga kanana da matsakaitan 'yan kasuwa da daidaikun mutane zai taimaka a samu karuwar kudaden hada hada wanda ke da muhimmanci wajen habaka kasuwanci da sayayyar kayayyakin amfanin gida na yau da kullum. Shi ma batun zurfafa sha'anin bude kofa ga kasahen waje ya dace, musamman yadda gwamnati ta ce za ta kara sassauta manufofin shiyyoyin raya tattalin arziki marasa shinge dake kasar Sin, duk matakai ne da za su kara zaburar da 'yan kasuwa su zo kasar Sin cinikayya ko zuba jari.

Na gode.

Mai sauraronku a kullum

Nuraddeen Ibrahim Adam

Birnin Tianjin, China

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China