lafiya1820.m4a
|
Kwanan baya, mujallar ilmin jinyar kananan yara ta kasar Amurka, ta kaddamar da sakamakon sabon nazari dake cewa, kananan yara da ba su yi dogon barci ba, sun fi fuskantar barazanar kamuwa da ciwon sukari nau'i na 2.
Kwalejin St George's ta jami'ar London ta kasar Birtaniya ce ta shugabanci wannan nazari, inda aka nuna cewa, an riga an tabbatar da cewa, ga baligai, yin dogon barci fiye da kima, ko kuma rashin isasshen barci, dukkansu suna da nasaba da kamuwa da ciwon kiba, da ciwon sukari nau'i na 2. Ga kananan yara kuwa, samun isasshen barci yana da nasaba da raguwar barazanar yin kiba. Amma babu isassun nazarce-nazarcen da aka gudanar kan alakar da ke tsakanin tsawon lokacin barci da kuma kamuwa da ciwon sukari mai nau'i na 2.
Don haka, masu nazarin sun tantance bayanan da suka shafi kananan yara 'yan Birtaniya fiye da dubu 4 da dari 5, wadanda shekarunsu suka wuce 9, amma ba su kai 10 a duniya ba, dangane da tsayin jikinsu, nauyin jikinsu, sakamakon binciken jininsu, da yadda su kan yi barci.
Sakamakon tantancewar ya shaida cewa, matsakacin tsawon lokacin barci da wadannan kananan yara su kan dauka suna yi a ko wane dare, daga ranar Litinin zuwa ta Jumma'a ya kai awoyi 10 da rabi, wanda ya cancanci shawarar da aka gabatar, wato a kalla awoyi 10 a ko wane dare. Galibi dai, idan tsawon lokacin barcin kananan yara yana karuwa, sai barazanar kamuwa da ciwon sukari da suke fuskanta ta rika raguwa.
Kamar yadda aka tabbatar a baya, karuwar tsawon lokacin barcin kananan yara yana da nasaba da raguwar barazanar yin kiba. Ban da haka kuma, ba a gano alaka a tsakanin tsawon lokacin barcin kananan yara da kuma barazanar kamuwa da cututtukan zuciya, da na magudanar jini ba.
Sakamakon haka, masu nazarin sun kiyasta cewa, karuwar tsawon lokacin barcin kananan yara, yana da nasaba da raguwar barazanar kamuwa da ciwon sukari nau'i na 2 da suka fuskanta. Amma suna bukatar ci gaba da nazarinsu kan dalilin da ya sa hakan.
Masu nazarin sun yi bayani da cewa, nazarinsu ya shaida mana cewa, watakila kara tsawon lokacin barci, zai taimaka a lalubo bakin zaren hanya mai sauki ta rage kibar da ke cikin jikin dan Adam, da kuma barazanar kamuwa da ciwon sukari nau'i na 2 a lokacin yarinta. (Tasallah Yuan)